Mamadou Sangaré, ya lashe kyautar Marc-Vivien Foé ta 2026 wadda ake ba wa ƴan wasan Afirka da ke wasa a gasar Ligue 1 ta Faransa, inda ya kafa tarihin kasancewa ɗan ƙasar Mali na farko da ya lashe wannan kyauta.
Ɗan wasan wanda wanda masoyin Seydou Keïta ne, wato tsohon ɗan wasan ƙasar Mali da Barcelona yana wasa ne a ƙungiyar ƙwalllon ƙafa ta RC Lens a ƙasar Faransa.
Mamadou Sangaré, wanda aka fi sani da « Gaucher » saboda gwanintarsa da kafar hagu, taso ne daga makarantar horar da kwallo ta Yeelen Olympique da ke Bamako, babban birnin Mali.
Hazaƙarsa ta fito fili ne sosai bayan komawarsa kungiyar RC Lens ta kasar Faransa daga Red Bull Salzburg ta kasar Austria a shekarar 2025, inda a cikin ƙanƙanin lokaci ya zama ɗaya daga cikin manyan matasan ‘yan wasa a gasar Ligue 1
Ga dai ƴan wasa uku na ƙarshe da Sangare ya yi takarar lashe wannan kyauta da su da ƙungiyoyin da suke buga wa:
Lamine Camara, yana bugawa a tsakiya ne da sunan (ASMonaco/Sénégal)
Shekarunsa 22 a duniya, Lamine Camara ya taka gagarumar rawa wajen ganin kulob ɗinsa na ya haska tsawon kakar wasanni uku jere da juna.
Moussa Niakhaté, yana tsaron baya a ƙungiyoyin (O.Lyonnais/Sénégal)
















